Skip to main content

Posts

Showing posts from December, 2025
One of the biggest financial lies people believe is that life will be easy when income increases. But the truth is simple: If you can’t manage small income, big income will stress you more. In Nigeria, many people earn small or irregular income. Yet, peace of mind is still possible, with the right system. 1. Understand Your Income Reality Small income means you must be intentional.  Know: • How much comes in • How often it comes • Where it mostly goes Write everything.  Even simple notes can change your money life. 2. Give Your Money a Job Before money enters your hand, decide: • This is for food • This is for transport • This is for savings 3. Save First, Not What Is Left Waiting to save leftovers rarely works. Saving small money first builds confidence and control. Even ₦500 saved is better than ₦0 planned. 4. Control Spending, Don’t Kill Enjoyment. Managing money doesn’t mean suffering. • It means: Saying no to unnecessary spending. • Choosing peace over pressure • Avoidin...
Na ga wannan rubutu da ke sukar wasu abubuwa a cikin fina-finan Hausa, musamman batun nuna wasu halaye da ake cewa ba su dace ba.  Gaskiya, wannan ra’ayi yana da kyau, amma a ganina akwai wani babban abu da muke mantawa da shi.  Wannan tsatstsauran ra’ayin ne ya hana fina-finan Hausa daukaka. Dalili kuwa shine: Fina-finai a ko’ina a duniya suna nuna zahirin abinda ke faruwa ne a rayuwa, mai kyau da mara kyau. Ba wai don su ƙarfafa mummunan hali ba, sai dai don su faɗakar, ko su nuna sakamakon aikata laifi, sai su koyar ta hanyar labari. Amma a nan, duk lokacin da aka taɓo wani abu na gaskiyar rayuwa: sai mu tashi muna cewa “Haram ne” “Bai dace ba” “Ana lalata tarbiyya” Daga ƙarshe Sai a takura marubuci, darakta da kuma jarumi.  Film fa ba wa’azi ba ne kai tsaye, labari ne da ke ɗauke da darasi a ƙarshe. Idan muka ci gaba da boye gaskiya, muna tilasta wa fina-finanmu zama a waje ɗaya, ba za su girma ba, balle kuma su fita cikin duniya. Abin da zai matuƙar baku mamaki kuwa ...
A cikin al’ummarmu, yanzun akwai wani abu da mutane da dama basu lura da shi ba, shi ne: matan da suke yin shigar banza ko saka kayan zamani sosai, sau da yawa suna samun miji da wuri fiye da masu shigar mutunci.  Amma abin tambayar me yasa hakan ke faruwa?  Bari mu ɗan yi nazari. Hangen Nesa da Kyawawan Hali: Maganar gaskiya Matan da ke saka suturun zamani don jawo hankalin maza sun fi ladabi a zahiri, tsari, da kuma kula da kansu. Ko a unguwar ku ka duba da kyau zaka ga wacce ake ganin bata jin magana tafi gaida manyan mutane. Su masu shigar mutumcin su da suke na gari gaskiyar magana zaka ga ba kowa suke gaidawa ba.  Wannan yana nuna cewa suna da hangen nesa da kyakkyawan hali a zahiri wanda zai saka namiji yaji yana so. Saukin Hulɗa ko mu'amala: Lokacin da mace ke fita cikin kwalliya tafi kyau da kwarjini, mutane da dama zasu fi lura da ita fiye da wacce bata yi ba.  Wannan yana bude mata damar yin hulɗa da mutane daban-daban, ciki har da wadanda...
A karon farko cikin shekaru 34, wata kasa cikin UN member ta amince da Republic of Somaliland a matsayin kasa mai ‘yanci da cikakken iko! 🇸🇴🤝🇮🇱 A yau (26 ga Disamba, 2025), Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu da Shugaban Somaliland Abdirahman Mohamed Abdullahi sun rattaba hannu na joint declaration wanda zai kafa cikakkiyar dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. Me yasa wannan lamari yake da muhimmanci?  Na farko dai shine: Somaliland ta ayyana ‘yancin kai tun 1991, amma duk da zamanta ƙasa Mai Mulkin demokradiyya, Cikin kwanciyar hankali na kusan shekaru 3, ba ta samu official recognition daga duniya ba har zuwa yau. Abraham Accords: Wannan matakin ana ganin shi extension na zama Abraham Accords. Somaliland ta nuna sha’awarta na shiga Accords a hukumance nan gaba.  Sabbin abokan Hulda: Za a samu hadin gwiwa kai tsaye a technology, agriculture, healthcare, har da bude embassies a Jerusalem da Hargeisa.  Sauyin Strategic: Wannan zai canza matsayin tsar...
Bayan shekaru 20 Google ya ba mu damar sauya Gmail address din mu. Shin ka tuna Gmail ɗinka na farko?  sk8er_boi2004, glitterprincess99, ko wani username mai ban dariya da ka yi amfani dashi lokacin buɗe Gmail?  Bayan shekara da shekaru kana amfani da shi, Well, Google ya kawo mana labari mai dadi: za ka iya canza primary Gmail ɗinka yanzu! 😱 Imagine yanzu zaka tura Gmail dinka ko ina, ba tare da jin kunya ba.  Kuma abu mafi ban sha'awa shine: Komai naka na nan ko da ka gyara username din : Google Photos, Drive files, YouTube subscriptions da sauran su ba za ka rasa komai ba. Tsofaffin saƙonninka ba zasu goge ba.  Sai dai akwai limit na editing din sunan,shine : Sau ɗaya a cikin shekara, gaba ɗaya kuma sau 3.  Don haka choose wisely! Don dubawa idan kana son gyarawa kashi ga  Google Account Settings > Personal Info > Email > Edit address Idan baka gani ba tukuna, kar ka damu ka sake gwadawa . #Gmail #TechNews #LifeHack
Samun mutane irinsu Barista Audu Bulama Bukarti hujja ce mai ƙarfi da ke nuna cewa Musulunci yana buƙatar wakilci a kowane fanni, musamman a media na duniya.  Idan batun tsaro ya taso a Arewa, shi ne manyan jaridun duniya ke gayyata domin sharhi—saboda ƙwarewarsa a doka, tsaro da diplomasiyya, da kuma yadda yake magana cikin ilmi, bincike da adalci. Gaskiya ita ce, kusan ya zama muryarmu, domin ba mu da media mai ƙarfi a Arewa da ke iya shiga duniya ta bayyana haƙiƙanin halin da muke ciki daga bakinmu.  Wannan gibi ne ya sa maƙiya ke fitar da labaran ƙarya a kanmu, duniya kuma ta yarda. Ana yaɗa cewa muna yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi, kuma ana karɓa—saboda ba mu da ƙarfin media da za ta fitar da gaskiya ta sa duniya ta saurare. Misali, shekaran jiya an kai hari a masallaci a Maiduguri, amma aka juya labarin aka ce Kiristoci aka kai wa hari a lokacin bikinsu—kuma duniya ta yarda. Gaskiyar magana itace: Muna buƙatar wakilci mai ƙarfi a media. Muna buƙatar “Bulamo...
Kenya ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta rattaba hannu kan wata babbar yarjejeniya da Amurka kan abinda ya shafi lafiyar jama’a (Health deal). Za su samu kuɗi, kayan aiki, sabbin fasahohin kiwon lafiya da tallafi. A cikin yarjejeniyar, Amurka za ta iya samun damar ganin bayanan lafiyar uk wani ɗan ƙasar, ciki har da rikodin ɗin asibiti , bayanan cututtuka , har ma da genomic data . Wato irin bayanan da suka fi kowane sirri a rayuwar mutum . Wasu rahotanni ma sun ce hakan yana iya ba da damar ganin sunayen mutane da wurin da suke karɓar magani, in real time. Duk da kuwa gwamnati ta ce za a bi dokar kariyar bayanai .  Wannan hadin gwiwa na iya inganta kiwon lafiya sosai. Mutane za su amfana da kayan aiki, rigakafi , ma’aikata, da ƙarin ƙarfin asibitoci. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, menene darajar sirrin mutane idan har ya koma hannun wata ƙasa? Kuma me yasa a Afrika duk lokacin da ake maganar “ development partnership ” sai bayanai na jama’a su fara shiga cikin kwan...
© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm