Samun mutane irinsu Barista Audu Bulama Bukarti hujja ce mai ƙarfi da ke nuna cewa Musulunci yana buƙatar wakilci a kowane fanni, musamman a media na duniya.
Idan batun tsaro ya taso a Arewa, shi ne manyan jaridun duniya ke gayyata domin sharhi—saboda ƙwarewarsa a doka, tsaro da diplomasiyya, da kuma yadda yake magana cikin ilmi, bincike da adalci.
Gaskiya ita ce, kusan ya zama muryarmu, domin ba mu da media mai ƙarfi a Arewa da ke iya shiga duniya ta bayyana haƙiƙanin halin da muke ciki daga bakinmu.
Wannan gibi ne ya sa maƙiya ke fitar da labaran ƙarya a kanmu, duniya kuma ta yarda. Ana yaɗa cewa muna yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi, kuma ana karɓa—saboda ba mu da ƙarfin media da za ta fitar da gaskiya ta sa duniya ta saurare.
Misali, shekaran jiya an kai hari a masallaci a Maiduguri, amma aka juya labarin aka ce Kiristoci aka kai wa hari a lokacin bikinsu—kuma duniya ta yarda.
Gaskiyar magana itace: Muna buƙatar wakilci mai ƙarfi a media. Muna buƙatar “Bulamomi” da za su fitar wa duniya muryarmu.
Haka kuma, akwai buƙatar ’yan kasuwa su zuba jari a harkar media—ba wai saboda wakilcin al’umma kaɗai ba, har da riba a ciki.
Allah Ya datar da mu.
#Raayi #Media #Wakilci #Arewa #Gaskiya #WeLearnEveryDay
Comments
Post a Comment