Skip to main content

Meyasa Matan Da Suke Yin Shigar Banza Suka Fi Samun Miji Da Wuri?

A cikin al’ummarmu, yanzun akwai wani abu da mutane da dama basu lura da shi ba, shi ne: matan da suke yin shigar banza ko saka kayan zamani sosai, sau da yawa suna samun miji da wuri fiye da masu shigar mutunci. 

Amma abin tambayar me yasa hakan ke faruwa? 

Bari mu ɗan yi nazari.

Hangen Nesa da Kyawawan Hali:
Maganar gaskiya Matan da ke saka suturun zamani don jawo hankalin maza sun fi ladabi a zahiri, tsari, da kuma kula da kansu. Ko a unguwar ku ka duba da kyau zaka ga wacce ake ganin bata jin magana tafi gaida manyan mutane. Su masu shigar mutumcin su da suke na gari gaskiyar magana zaka ga ba kowa suke gaidawa ba. 

Wannan yana nuna cewa suna da hangen nesa da kyakkyawan hali a zahiri wanda zai saka namiji yaji yana so.

Saukin Hulɗa ko mu'amala: Lokacin da mace ke fita cikin kwalliya tafi kyau da kwarjini, mutane da dama zasu fi lura da ita fiye da wacce bata yi ba. 

Wannan yana bude mata damar yin hulɗa da mutane daban-daban, ciki har da wadanda za su iya zama abokan rayuwarta.

Sannan kuma muna wani zamani da Yin shigar zamani ko kayan banza yana nufin mace tana kulawa da kanta, tana da tsafta, tana gyara jiki, kuma tana son zama cikin koshin lafiya. 

Ko mun ƙi ko mun so Wannan yana kara mata daraja a idanun mutane.

 Wannan ba ina ƙarfafa shigar banza Ba ne, a'a ina faɗar abin da yake zahiri ne.

 Shi samun miji a ba'a shigar banza yake ba, bari dai kawai Akwai halaye, tarbiyya, tunani, da yadda take mu’amala da mutane da suke da tasiri sosai.

Shigar banza wani abu ne kawai daga cikin abubuwan da ke kara jan hankali, amma kyakkyawan hali da tarbiyya sune ginshikin aure mai dorewa.

Kuma kunyar mutane da ƙin yi masu magana bashi zai sa su gane ke mutumniyar kirki bace.

Daga Karshe ba ina goyon bayan shigar banza Ba ne. Kuma bani NA Mata shawarar su koma shigar banza, sai zan ɗan ja hankalinsu da su riƙa gaida manyan mutane, da yayayunsu na unguwa, domin kuwa sune ake tambaya halayensu in aka zo neman aurensu.

Duk kyawun halinki idan baki mu'amala mai kyau da yan unguwar ku ba lallai ki samu shaida mai kyau daga gare su ba.

We learn everyday 

#Mata #ShigarBanza #Soyayya #Aure #HaliMaiKyau #Rayuwa

Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm