Skip to main content

Kenya da US Health Data Deal — Abin Da Yake Faruwa Karkashin Kasa

Kenya ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta rattaba hannu kan wata babbar yarjejeniya da Amurka kan abinda ya shafi lafiyar jama’a(Health deal). Za su samu kuɗi, kayan aiki, sabbin fasahohin kiwon lafiya da tallafi.


A cikin yarjejeniyar, Amurka za ta iya samun damar ganin bayanan lafiyar uk wani ɗan ƙasar, ciki har da rikodin ɗin asibiti, bayanan cututtuka, har ma da genomic data. Wato irin bayanan da suka fi kowane sirri a rayuwar mutum.

Wasu rahotanni ma sun ce hakan yana iya ba da damar ganin sunayen mutane da wurin da suke karɓar magani, in real time. Duk da kuwa gwamnati ta ce za a bi dokar kariyar bayanai.

 Wannan hadin gwiwa na iya inganta kiwon lafiya sosai. Mutane za su amfana da kayan aiki, rigakafi, ma’aikata, da ƙarin ƙarfin asibitoci.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, menene darajar sirrin mutane idan har ya koma hannun wata ƙasa?

Kuma me yasa a Afrika duk lokacin da ake maganar “development partnership” sai bayanai na jama’a su fara shiga cikin kwangila?

A gaskiya, ƙasashen nan masu ƙarfi suna gina arzikin su ne da bayanai, ba da ma’adinai kawai ba. Kuma Afrika na shiga ba tare da rigar kariya ba.

Yanzun dai Kenya ta fara. Sauran ƙasashen Afirka za su biyo baya.

Tambayar ita ce: shin Wannan fadada lafiyar jama’a ne, ko kuma sayar da sirrin jama’a da sunan ci gaba?

We learn every day.

Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm