Bayan shekaru 20 Google ya ba mu damar sauya Gmail address din mu.
Shin ka tuna Gmail ɗinka na farko?
sk8er_boi2004, glitterprincess99, ko wani username mai ban dariya da ka yi amfani dashi lokacin buɗe Gmail?
Bayan shekara da shekaru kana amfani da shi, Well, Google ya kawo mana labari mai dadi: za ka iya canza primary Gmail ɗinka yanzu! 😱
Imagine yanzu zaka tura Gmail dinka ko ina, ba tare da jin kunya ba.
Kuma abu mafi ban sha'awa shine: Komai naka na nan ko da ka gyara username din : Google Photos, Drive files, YouTube subscriptions da sauran su ba za ka rasa komai ba.
Tsofaffin saƙonninka ba zasu goge ba.
Sai dai akwai limit na editing din sunan,shine : Sau ɗaya a cikin shekara, gaba ɗaya kuma sau 3.
Don haka choose wisely!
Don dubawa idan kana son gyarawa kashi ga
Google Account Settings > Personal Info > Email > Edit address
Idan baka gani ba tukuna, kar ka damu ka sake gwadawa .
Comments
Post a Comment