Na ga wannan rubutu da ke sukar wasu abubuwa a cikin fina-finan Hausa, musamman batun nuna wasu halaye da ake cewa ba su dace ba.
Gaskiya, wannan ra’ayi yana da kyau, amma a ganina akwai wani babban abu da muke mantawa da shi.
Wannan tsatstsauran ra’ayin ne ya hana fina-finan Hausa daukaka.
Dalili kuwa shine: Fina-finai a ko’ina a duniya suna nuna zahirin abinda ke faruwa ne a rayuwa, mai kyau da mara kyau. Ba wai don su ƙarfafa mummunan hali ba, sai dai don su faɗakar, ko su nuna sakamakon aikata laifi, sai su koyar ta hanyar labari.
Amma a nan, duk lokacin da aka taɓo wani abu na gaskiyar rayuwa: sai mu tashi muna cewa “Haram ne” “Bai dace ba” “Ana lalata tarbiyya”
Daga ƙarshe Sai a takura marubuci, darakta da kuma jarumi.
Film fa ba wa’azi ba ne kai tsaye, labari ne da ke ɗauke da darasi a ƙarshe. Idan muka ci gaba da boye gaskiya, muna tilasta wa fina-finanmu zama a waje ɗaya, ba za su girma ba, balle kuma su fita cikin duniya.
Abin da zai matuƙar baku mamaki kuwa shine: Yaran dai da ba'a so su lalace dalilin kallon Film ɗin Hausa, zaka same su suna kallon Netflix, Indian Hausa,YouTube, da TikTok.
Amma kuma da an dawo kan Film din Hausa sai a fara wa'azi.
Gaskiyar magana Idan har muna son Fina-finan Hausa su yi gogayya a duniya, Su ja hankalin matasa, Su samu cigaba da kudi, To dole mu bar marubutanmu su rubuta gaskiya cikin hikima, Sannan kuma mu daina tsorata su da sunan al’ada ko addini.
Ci gaba ba ya zuwa ta hanyar boye gaskiya. Cigaba Yana zuwa ne ta fuskantarta cikin basira.
We learn every day.
Comments
Post a Comment