Skip to main content

Yadda Ake Magance Coccidiosis A Gargajiyance

Yadda Ake Magance Coccidiosis A Gargajiyance

Idan kana kiwon kaji, wannan post ɗin yana da muhimmanci gare ka.

Coccidiosis na daga cikin manyan cututtukan da ke kashe kananan kaji.

 Cuta ce da ƙananan parasites ke haddasawa, suna kama hanjin kaji. Yana yaɗuwa ta kashinsu mai ɗauke da cutar da kuma ruwan shan da ya gurɓata.

Yaya zaka gane kajinka na da cutar?

Ka lura da waɗannan alamomi: Zawo mai jini ko ruwa-ruwa, Rashin cin abinci,   Rauni da kasala, Rage nauyi,  Launin kunya ko farar fata a kan kai, Yawan mutuwar kaji.

Idan ka ga waɗannan alamomi, ka yi gaggawa. Kada ka yi sakaci wajen neman magani.

 MAGANIN DA ZAKA IYA HAƊAWA A GIDA 

1. Ruwan Tafarnuwa

Ka daka tafarnuwa ka saka ta a ruwan shan kaji.

 Bincike ya nuna tafarnuwa tana taimakawa wajen rage cutar coccidiosis.

2. Apple Cider Vinegar

Ka saka cokali 1 zuwa 2 na vinegar  a kowace lita 4 na ruwa. Yana taimaka wa lafiyar hanji da hana yawaitar parasites.

3. Oregano

Ka haɗa oregano foda a abincin kaji — kusan gram 2 zuwa 3 a kowace gram 100 na feed. Yana da ƙarfin kashe ƙwayoyin cuta da parasites.

4. Turmeric (Kurkum)

Ka saka turmeric a abincin kaji kullum. Yana rage lalacewar hanji kuma yana taimaka wa kaji su warke da sauri.

5. Shayin Green Tea ko Oregano

Ka dafa shayi na green tea ko oregano, ka bar shi ya huce, sannan ka ba kaji su sha. Yana da matuƙar amfani musamman ga kananan kaji.

6. Ginger (Jinja)

Ka saka fodar ginger a abinci domin taimaka wa narkewar abinci da ƙarfafa garkuwar jiki.

KARIYA DAGA CUTAR ITA CE ABU  MAFI KYAU 

- Ka tsaftace muhallin su kullum
- Kada ka bari kaji su yi cunkoso wuri guda 
- Sauya ruwan sha kowace rana
- Ka riƙa saka tafarnuwa da vinegar a ruwa a matsayin kariya

Wadannan hanyoyi suna aiki sosai wajen kariya daga ƙananan matsaloli. 

Idan kajinka suna mutuwa da yawa, ka nemi likitan dabbobi cikin gaggawa. Kada ka yi wasa da rayuwar kajinka

Ku biyo wannan shafi domin samun ƙarin shawarwarin kiwon kaji

Ka taɓa fuskantar coccidiosis a  kajinka? 

Da me kayi amfani?

We learn every day 
#KiwonKaji #Coccidiosis #OrganicFarming #MasuKiwonKaji #LafiyarKaji #NomaNaHalitta #NigeriaFarmers

Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm