Skip to main content

Shin Ka taɓa siyan kaji saboda suna burge ka kawai ka kiwata, amma daga baya sai ka gane ba su dace da abin da kake so ba?

Shin Ka taɓa siyan kaji saboda suna burge ka kawai ka kiwata, amma daga baya sai ka gane ba su dace da abin da kake so ba?

Yawancin masu fara kiwon kaji suna yin babban kuskure. Suna zuwa hatchery su sayi kaji kawai saboda sun ga sun yi masu kyau ko kuma wani ya ce masu su masu kyau ne. Su kuma sai su suyi ba tare da bincike ba.

Amma a gaskiya, kafin ka sayi kaji, dole ka fara sanin manufarka. Mi kake so? Nama ko kwai? 

A kiwon kaji akwai manyan rukuni guda uku: Layers, Broilers da waɗanda ake cewa '' Dual-purpose.

Bari muyi ɗan gajeren bayani akan kowane daga cikin ukkun:

 Layers
Waɗannan kaji ana kiwon su ne domin ƙwai. Misalai sun haɗa da Rhode Island Red da Leghorns. Idan kana son samun kuɗi na dogon lokaci daga ƙwai, waɗannan su ne suka fi dacewa.

 Broilers
Waɗannan kuma ana kiwon su ne domin nama. Suna girma da sauri sosai. Idan kana son kasuwanci mai saurin kawo riba, broilers su ne zabinka.

 Dual-Purpose
Su ne kaji da ake iya amfani da su domin ƙwai da nama. Kamar Plymouth Rock. Su ne a tsakiyar hanya ga wanda yake son haɗa duka biyun.

Daga ƙarshe Gaskiyar dai ita ce:
Idan baka san dalilin da yasa kake kiwon kaji ba, zaka iya yin asara ba tare da ka sani ba. Amma idan ka fara da manufa mai kyau, zaka fi samun riba kuma kajinka zasu fi bada sakamako mai kyau.

Idan kana shirin fara kiwon kaji, ka fara tambayar kanka kamar haka:Ina son ƙwai ne? Ina son nama ne? Ko kuma dai ina son duka biyun?


We learn every day.


Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm