Kana tunanin kiwon kaji aiki ne da zaka yi ka barshi? Ba haka ba ne!
Jama'a Kiwon kaji fa yana buƙatar kulawa kullum. Idan baka kula da su yau ba, zaka iya fuskantar asara gobe. Idan kana shirin shiga wannan harka, to ka sani ga abin da fa zaka rika yi nan a kullum:
1- Da Safe (Morning)
Ka fito da kaji su samu iska da motsa jiki.
Ka canza musu ruwa – wannan yana da matuƙar muhimmanci!
Ka basu abinci mai kyau domin su samu kuzari.
2- Rana Tsaka (Afternoon)
Idan kajinka masu yin ƙwai ne, ka tattara ƙwai.
Wannan zai taimaka wajen rage ɓarna da kuma tsafta.
3- Da Yamma (Evening)
Ka mayar da kaji cikin gidansu, sannan ka rufe wurin sosai saboda tsaro.
Ka duba kaji domin ganin ko akwai wanda yake rashin lafiya ko rashin kuzari acikin su. Idan akwai ka ware shi.
Nasara a kiwon kaji tana zuwa ne daga irin kulawar da ake masu kullum.
Ƙananan abubuwan nan da kake yi a kullum rana sune ke kare kajinka da kuma baka riba daga ƙarshe.
Idan kana shirin fara kiwon kaji, ka tabbata kana da lokaci da juriyar kula da su kullum.
We learn every day.
Comments
Post a Comment