Kana son fara kiwon kaji acikin gida? Tsaya ka karanta wannan to...
Yin kuskure a waɗannan abubuwa guda 5 na iya jawo maka asara… har ma da mutuwar kajin ka.
Yawancin sabbin masu fara kiwon kaji, suna farawa ne cikin farin cikin yau suma sun fara kiwon Kaji.
Sai kawai suje su sayi ƙananan kaji (Daya old). Su sami kwali ko su saka ayi masu keji. Shikenan sun zama masu kiwon kaji🙄
Amma gaskiyar ita ce, kiwon kaji ba saye kawai ba ne… shiri ne. Sai an shirya mashi. Shirin kuma sosai.
Ga wasu abubuwa 5 da dole ka tanade su kafin ka sayi kaji:
1. Wuri mai kyau (Housing)
Dole kaji su samu wuri wanda zai basu kariya daga rana, sanyi da kuma ruwa. Idan muhalli bai dace dasu ba, kajin ka suna iya mutuwa cikin sauƙi. Ba tare da ka farga ba.
2. Zafi ga ƙananan kaji (Heat Source)
'' Day Old '' ba sa iya jure sanyi. Kana buƙatar brooder ko fitila mai bada zafi domin su rayu cikin koshin lafiya a farkon rayuwarsu.
3. Abinci mai inganci (Quality Feed)
Abincin kaji yana da matuƙar muhimmanci. Rashin ingantaccen abinci yana iya hana kaji girma ko haifar masu da cututtuka.
4. Ruwa mai tsafta (Clean Water)
Kaji suna buƙatar ruwa mai tsafta kullum. Ruwa mai datti na iya jawo masu cututtuka da wuri.
5. Tsaro daga cutarwa daga dabbobin da ke iya farautarsu (Health & Safety)
Dole ka tabbatar kajinka suna cikin tsaro daga cututtuka, beraye, mage, ko sauran dabbobin da ka iya cutar da su.
Daga ƙarshe dai a gaskiya yawancin matsalolin kiwon kaji suna faruwa ne saboda rashin shiri kafin saye.
Idan ka fara da shiri mai kyau insha'allahu, zaka rage asara ko da ta zo, sannan kuma, ka samu riba.
Idan kana son fara kiwon kaji, ka tabbatar ka tanadi waɗannan abubuwa 5 kafin ka sayi ''Day Old''.
We learn every day.
Comments
Post a Comment