Skip to main content

Kajinka ba sa buƙatar wani kyale-kyalen gida/keji da za'a kashe kuɗi, amma dai tabbas suna buƙatar gidan da zai basu tsaro!

 Kajinka ba sa buƙatar wani kyale-kyalen gida/keji da za'a kashe kuɗi, amma dai tabbas suna buƙatar gidan da zai basu tsaro!

Yawancin masu kiwon kaji suna mayar da hankali kan abinci ne da sayen kaji, amma kuma suna mantawa da muhalli. 

Gaskiyar ita ce, gidan kaji mai kyau na iya ceton rayuwar kajinka da kasuwancinka.

Domin gidan kaji ya zama mai kyau, dole ya ƙunshi abubuwan nan guda uku:

 1. Tsaro (Security)

Gidan kaji dole ya kare su daga baƙin da ba'a aikawa gayyata ba, kamar karnuka, mage, beraye ko sauran dabbobin da ke iya kashe kaji.

Idan babu tsaro mai kyau, zaka iya rasa kajinka cikin dare ɗaya.

 2. Iska mai kyau (Ventilation)

Kaji suna fitar da ammonia, wanda kuma zata iya cutar da lafiyarsu.

 Saboda haka dole gidan kajinka ya kasance yana samun iska mai kyau.

 Rashin iska mai kyau yana iya jawo cututtuka da mutuwar kaji.

 3. Isasshen fili (Space)

Cunkoso yana janyo damuwa da cututtuka ga kaji. In San samu ne, ana so:

 A cikin gida: Ka tanadi kusan square feet 3 zuwa 4 ga kowace kaza.

A waje kuma (run): Ka tanadi kusan square feet 10 ga kowace kaza.


Idan kaji suna rayuwa a muhalli mai kyau, suna girma cikin koshin lafiya, sannan kuma su bada sakamako mai kyau, sannan kuma idan asara ta zo cikin ikon Allah ba za'a yi da yawa ba.

Kiwon kaji ba wai kawai ciyarwa ba ne… muhalli mai kyau shi ne ginshiƙin samun nasara.



We learn every day.


Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm