Skip to main content

Jadawalin Abincin Kaji Na Musamman

Yawancin masu kiwon kaji suna tunanin saboda basu da kaji da yawa to ba su buƙatar abinci na musamman saboda yana da tsada, amma gaskiya ita ce, kaji komai rashin yawansu, suna buƙatar abinci na musamman gwargwadon shekarunsu. 

Wannan zai taimaka musu su girma cikin koshin lafiya da bada sakamakon da ake so mai kyau.

Ga wani jadawali da nayi bincike na fitar na yadda ake ciyar da kaji bisa matakan rayuwarsu:

Daga kwana daya 1 zuwa sati 8 (8Weeks ) Ƙananan kaji a riƙa basu '' Starter Crumbles''

Wannan abinci yana da protein mai yawa wanda yake taimaka wa kaji su girma da sauri da kuma kuzari a farkon rayuwarsu.

Daga sati 8 zuwa sati 20 kuwa Matasa kaji kenan a riƙa basu '' Grower Feed ''

Yana taimaka musu sosai wajen ci gaba da girma cikin daidaito har su kai lokacin balaga.

Daga sati 20 Weeks zuwa sama kuwa (Kaji masu yin ƙwai)
'' Layer Pellets ''

Wannan abinci yana ɗauke da calcium wanda yake taimaka wa kaji su yi ƙwai masu ƙarfi.

Ya kai Ɗan uwa ko Yar uwa mai Kiwon Kaji, ka sani '' Ingantaccen abinci yana rage cututtuka, yana sa kaji su girma cikin koshin lafiya, kuma yana ƙara yawan riba a kiwon kaji '' .

Idan kana son kajinka su maka yanda kake so cikin ikon Allah, kada ka dogara da sauƙin abincin kaji kawai wajen saye. Ka tabbata kana basu abinci da ya dace da shekarunsu.

Ka ajiye wannan post domin amfani a gaba.

We learn every day.

#kiwonkajinhausaazamanance #virals #broiler #chicken #layers

Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm