Skip to main content

Elon Musk Da AI

A daren jiya ina zaune inata scrolling as usual a Twitter, sai na ci karo da wani post na Elon Musk da ta sa na tsaya cak. Ba wai saboda tsoron abin da ya faɗa ba ne, sai don gaskiyar da ke cikin abun da ya fada.

Ya ce: “AI da robotics kamar guguwa(tsunami )ce mai saurin wuce tunani. Wannan shi ne canji mafi tsanani ko tsauri(radical) da duniya ta taɓa gani.”

Sai na ɗaga kai na, na kalli sararin samaniya na fara tunani. Na fara tuna lokacin da waya take don kira da SMS kawai. 

A Yau kuwa, waya takai tana tunani tare da mu, tana ba mu shawara, tana rubuta mana magana, tana zana mana hoto, tana koyar da mu abunda ba mu iya ba.

Abin da ya fi ban tsoro shi ne: wannan canji bai tsaya jirana ba. Bai tambaye Ni ko na shirya ba. Ya zo ne da gudu, kamar ambaliyar ruwa mai ƙarfi. 

Wasu suna kallonsa a matsayin wasa, wasu kuma suna ganin ba zai shafe su ba. Amma tarihi ya tabbatar mana da cewa duk wanda ya raina canji, canjin kan raina shi.

AI ba wai kawai na Turawa ko manyan ƙasashe ba ne. Yana nan zuwa gidanka. Sannan ya bika zuwa wajen aikinka. Zai kuma shiga cikin ilimin ’ya’yanka. 

Tambayar ba ita ba ce ta ko zai shafe mu ba; tambayar ita ce: ta wace hanya zai shafe mu?

Shin za mu kasance daga cikin waɗanda canjin ya ɗaga, ko kuma daga cikin waɗanda ya watsar ya bari a baya?

Elon Musk ya yi gargadi. Amma gargadi ba abin tsoro ba ne, kira ne domin farkawa.

Duniya dai na ta canzawa. Mu kuma fa?

We learn every day.

Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm