Wani lokaci zaka riƙa jin, ko ganin kamar ana amfani da wasu kalmomi masu wahalar fahimta, a harkar kiwon kaji? To ka sani ba kai kaɗai ba ne!
Yawancin sabbin fara kiwon kaji sukan shiga ruɗani idan suka ji an ambaci wasu kalmomi irin su Brooder, Pullet ko Pastured.
Saboda haka ga wani ɗan ƙaramin “Chick-tionary”😆 wato ma’anar kalmomin da duk wani mai kiwon kaji ya kamata ya sani.
Ka ajiye wannan post din domin zai taimaka maka sosai a nan gaba.
📦 Brooder
Wani Wuri ne ko akwatin da ake rainon ƙananan kaji (Daya old) inda suke samun zafi kamar jikin uwa da kuma kariya a farkon rayuwarsu.
🐣 Pullet
Matashiyar kaza wacce bata fara yin ƙwai ba tukuna, yawanci tana tsakanin watanni kaɗan zuwa lokacin da zata fara yin ƙwai.
🌿 Pastured Chickens
Kaji ne da ake saki suyi kiwo da kansu a waje. Suna samun damar yawo da cin ciyawa ko kwari a kasa. Ba da jiran sai an basu abinci. Sun iya nema. Sune dai muke kira da kajin Hausa.
🥚 Layer
Kazar da aka kiwo musamman domin yin ƙwai.
🍗 Broiler
Kazar da aka kiwo domin nama, suna girma da sauri sosai.
Sanin waɗannan kalmomi zai taimaka maka ka fahimci harkar kiwon kaji sosai, kuma zai ƙara maka ƙarfin gwiwa lokacin da kake koyon sabbin abubuwa ko tattaunawa da sauran masu kiwo.
We learn every day.
Comments
Post a Comment