Ba duk abokan gaba na kaji ake iya gani ba… wasu cututtuka a ɓoye suke.
Yawancin masu kiwon kaji suna tsoron karnuka ko beraye, amma gaskiyar ita ce cututtuka na iya kashe duk kajinka cikin lokaci kaɗan idan ba ka yi taka tsantsan ba.
Ga wasu hanyoyina Bio-Security domin kare kajinka:
1. Ka tanadi takalman da zaka rika shiga gidan kaji ko inda kajin ka suke (Coop Shoes)
Ka rika amfani da takalmi na musamman idan zaka shiga wurin kaji. Wannan yana hana shigar ƙwayoyin cuta daga waje.
2. Ware sabbin kaji (Quarantine)
Idan ka sayi sabbin kaji, ka ware su na tsawon kwanaki 30 kafin ka haɗa su da sauran kajinka.
Wannan zai taimaka maka wajen tabbatar da ba su da cuta.
Ku sani Bahaushe yace '' Rigakafi ya fi magani '' sau dubu.
Idan ka kula da tsafta da tsaro, zaka kare kajinka daga cutuka, sannan na zakai asara mai yawa ba.
Kiwon kaji ba ciyarwa kawai ba ne… kare su daga cuta yana daga cikin sirrin nasara.
We learn every day.
Comments
Post a Comment