Skip to main content
Ƙananan kaji(Day Old) ba kawai kaji ba ne su kamar saura, a'a suna buƙatar kulawa ta musamman kamar jarirai!

Yawancin kaji (Day Old) suna mutuwa a makonni na farko ba wai saboda cuta ba, sai saboda rashin kulawar da ta dace. Ka sani a wannan lokaci ne, kaji suka fi rauni fiye da kowane lokaci.

A cikin makonni 6 na farko, kai ne kamar uwarsu. Duk abinda uwar zata yi masu shi zaka yi masu. 

Ga wasu abubuwan da zaka tanada da zasu taimaka maka wajen kulawa da su:

 1. Brooder (akwatin rainon kaji)

Wannan shi ne wurin da chicks zasu zauna a farkon rayuwarsu. Dole ya kasance mai tsabta, mai kariya daga sanyi, iska mai ƙarfi da sauran haɗari.

 2. Zafi (Heat Lamp)

Ƙananan kaji ba sa iya jure sanyi.

A mako na farko, ya kamata zafin wurin ya kai kusan 35°C (95°F).

 Daga baya ana rage zafin a hankali yayin da suke girma.

 3. Abincin kaji( Day Old) Starter

Chicks suna buƙatar abinci mai ƙarfi da protein domin su girma cikin koshin lafiya. 

Rashin ingantaccen abinci yana iya hana su girma ko ya jawo masu cututtuka.

Yawancin nasarar kiwon kaji tana farawa ne tun daga yadda ka kula da su tun suna ƙanana.

 Idan suka fara rayuwa cikin koshin lafiya, zasu samu damar girma su zama kaji masu ƙarfin jiki, sannan su baka riba.

Idan kana shirin fara kiwon kaji, ka tabbata ka shirya kowane mataki,daga cikin matakai, sosai kafin ma ka kawo chicks din gida.


We learn every day.



Comments

© 2018 Jamilu Tukur Observer Design by Danteizm