Gaskiya na dade ina jiran irin wannan rana.
Duk lokacin da aka ambaci Maitatsine, yawancin abin da muke tunawa shi ne labarin da aka gada kawai,wanda ke cike da jita-jita, ba tare da cikakken bincike ba.
Sunan Marwa ya zama abin tsoro, amma kaɗan ne ke tambayar: me ya faru a zahiri? me ya kai shi ga haka? waye ya yi kuskure?
A kwanakin nan na ci karo da bayanan da ke yawo a online cewa an kammala dukkanin takardun doka da izini domin fara fim ɗin MAITATSINE. Wannan ya nuna cewa aikin ba jita-jita ba ne, an shirya shi cikin tsari, kuma za'a fara producing din shi nan ba da jimawa ba.
Abin da yafi ɗaukar hankalina shi ne cewa wannan fim ɗin zai waiwayi rikicin ’Yan Tatsine na shekarun 1980–1985, wanda ya shafi Kano, Maiduguri, Yola da Gombe, wato lokacin da ya girgiza Arewa da Najeriya gaba ɗaya. Wannan wani bangare ne na tarihinmu da har yanzu tasirinsa yana nan.
A cewar bayanan da aka wallafa, aikin babban ne, sama da mutane 3,000 za su shiga tsakanin cast da crew. Wannan kadai ya nuna cewa an dauki lamarin da muhimmanci, ba wasa aka zo yi ba.
Za'a gudanar da fim ɗin ne ƙarƙashin Prince Daniel Aboki, kuma mutane da dama suna sa ido don ganin yadda za a gabatar da wannan tarihi mai sarkakiya.
Ba wai don tayar da tsohon rauni ba, sai don fahimtar da al'umma gaskiyar tarihin.
Domin al’umma ba ta koyon darasi sai tana kallon tarihinta.
Comments
Post a Comment